logo

HAUSA

Shugaban Comoros ya alkawarta hada kan 'yan kasa

2024-05-27 09:50:22 CMG Hausa

Shugaban kasar Comoros Azali Assoumani, ya sha alwashin hada kan 'yan kasa da goyon bayan ci gaban ta. Shugaba Azali ya bayyana hakan ne cikin jawabin sa na shan rantsuwa a jiya Lahadi a birnin Moroni fadar mulkin kasar ta Comoros.

Shugaba Assoumani ya ce "A matsayina na shugaban janhuriyar Comoros, mai kare hukumomin kasa, kuma jami'i na farko mai kare moriyar kasa, zan yi duk mai yiwuwa wajen tabbatar da kare zaman lafiya, tsaro, da hadin kai da martabar yankunan kasar mu".

An sake zabar Assoumani a matsayin shugaban kasa a zagayen farko na babban zaben kasar Comoros da ya gudana a ranar 14 ga watan Janairun shekarar bana. Sakamakon karshe na zaben da kotun kolin kasar ta fitar ya nuna cewa, Azali ya lashe kaso 57.02 bisa dari na jimillar kuri’un da aka kada.

Bisa gayyatar da shugaba Assoumani na Comoros ya yi masa, He Baoxiang, wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci bikin rantsar da shugaban na Comoros.  (Saminu Alhassan)