Shugabancin JKS ya nazarci matakan gaggauta raya yankin tsakiyar kasar da kare hadarin harkokin kudi
2024-05-27 21:21:58 CMG Hausa
Shugabancin Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) ya tattauna kan manufofi da matakan gaggauta raya yankin tsakiyar kasar Sin a sabon zamani, tare da tanadin dokokin da suka shafi gazawa wajen daukar alhakin karewa ko magance hadarin harkokin kudi.
Sakatare janar na kwamitin kolin JKS Xi Jinping ne ya jagoranci zaman, wanda ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS ya gudanar a yau Litinin.
Taron ya bukaci a kara kokarin samun manyan nasarori wajen gaggauta raya yankin tsakiyar kasar Sin, da ya kunshi 1 bisa 10 na yankunan kasar, kuma mai kimanin rubu’i daya na al’ummar kasar. Haka kuma, ya bayyana yankin a matsayin mai muhimmanci ta fuskar samar da hatsi da makamashi da kayayyakin da ake sarrafawa da kere-keren kayayyakin aiki na zamani da masa’antar fasahohin zamani, haka kuma ta kansance wata cibiyar sufuri a kasar.
Taron ya kuma bukaci a nace ga neman ci gaba ta hanyar kirkire-kirkire da inganta binciken kimiyya da fasaha na hakika, domin samun nasarori. (Fa’iza Mustapha)