Iran ta sha alwashin ba da gudummawa ga 'yanci da ci gaban kasar Sudan in ji shugaban rikon kwaryar kasar
2024-05-27 11:11:16 CMG Hausa
Shugaban rikon kwarya a kasar Iran Mohammad Mokhber, ya ce kasarsa za ta yi duk abun da ya dace wajen baiwa al'ummar Sudan gudummawar kaiwa ga 'yanci, da ci gaba da samun zaman lafiya.
Wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizo na ofishin shugaban kasar Iran, ta ce shugaba Mokhber ya bayyana alwashin ne a jiya Lahadi, yayin da yake zantawa da mukaddashin ministan harkokin wajen Sudan Hussein Awad Ali a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran.
Yayin zantawar ta su, Mokhber ya tabo batu kan rawar da marigayi shugaban Iran Ebrahim Raisi, da ministan harkokin wajen sa Hossein Amir-Abdollahian suka taka a baya, a fannin ingiza alaka, da hadin gwiwar Musulmi da kasashe masu kaunar zaman lafiya, yana mai jaddada cewa, Iran za ta ci gaba da bin wannan tafarki, a matsayin sa na jigon cimma nasarar da aka sanya gaba.
A nasa bangare kuwa, Hussein Awad Ali cewa ya yi alakar kasarsa da Iran, ta ginu ne karkashin kawance Musulunci da manufofin jin kai, da ma abota tsakanin al'ummun sassan biyu.
A watan Oktoban bara, Iran da Sudan suka sanar da maido da huldar diflomasiyyar su, wadda ta katse tsawon shekaru 7. Sudan ta katse dangantaka da Iran ne a shekarar 2016, bayan da kasar Saudiyya ita ma ta kawo karshen alakarta da Tehran din a wannan shekara. (Saminu Alhassan)