Firaministan Sin ya bukaci Sin da Japan da Koriya ta Kudu da kada su amince da kutsen wasu kasashe cikin dangantakarsu
2024-05-27 21:20:31 CMG Hausa
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya yi kira ga kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu, da su yi kokari wajen adawa da duk wani tsaiko da za a kawowa dangantakarsu daga waje, kana sun nace ga zaman jituwa tare, da mara baya ga juna.
Li Qiang ya bayyana haka ne yayin taro kan harkokin kasuwanci karo na 8, tsakanin Sin da Japan da Koriya ta Kudu, wanda aka yi yau Litinin a birnin Seol.
Firaministan na Sin ya yi fatan ‘yan kasuwa za su kasance masu kare gudanar harkokin masana’antu da tsarin samar da kayayyaki na duniya cikin aminci ba tare da tangarda ba. (Fa’iza Mustapha)