Shugabannin Bahrain da Masar da Tunisiya da UAE za su ziyarci kasar Sin
2024-05-27 10:33:06 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta sanar da cewa, sarkin Bahrain Hamad bin Isa Al-Khalifa, da shugaban kasar Masar Abdul Fatah Al-Sisi, da kuma shugaban kasar Tunisiya Kais Saied, kana da shugaban hadaddiyar daular Larabawa wato UAE Mohamed Bin Zayed Al-Nahyan, za su ziyarci kasar Sin daga ranar 28 ga watan nan da muke ciki zuwa ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa, tare da halartar bikin bude taron ministoci karo na 10, na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da kasashen Larabawa. (Amina Xu)