Matashin da ya gaji aikin tsoffinsa na kare kwararar Hamada
2024-05-26 21:34:22 CRI
In an tashi daga gundumar Gulang ta lardin Gansu da ke arewa maso yammacin kasar Sin, aka doshi arewa, to za a isa wani gandun daji da ake kira Babusha, inda a bakin kofar shiga gandun, za a ga wani babban itacen da ya fi sauran bishiyoyin da ke kewaye tsayi, itacen da wasu tsofaffi guda shida suka dasa yau sama da shekaru 40 da suka wuce, wanda yanzu ya zama alamar yadda tsofaffin suka dukufa wajen kare kwararowar hamada a wurin.
To, a cikin shirinmu na yau, za mu gutsura muku labarin yadda zuriyoyin mutanen wurin suka dukufa wajen kare kwararowar hamada.(Lubabatu)