logo

HAUSA

An tsawaita wa’adin mulkin soja a Burkina Faso da shekaru 5

2024-05-26 17:21:53 CMG Hausa

Hukumomin soji a Burkina Faso, za su kasance kan mulki tsawon wasu karin shekaru 5, bayan mahalarta taron tattauna batutuwan kasa da aka yi a jiya Asabar, sun gabatar da shawarar tsawaita komawa tsarin demokradiyya da watanni 60, daga watan Yuli.

Wannan na kunshe ne cikin wani daftarin sabuwar dokar da aka amince da ita.

Hukumomin soji da suka yi juyin mulki a shekarar 2022 sun yi alkawarin gudanar da zabuka a watan Yulin bana domin mayar da mulki ga farar hula, sai dai hakan ya dogara ne da yanayin tsaro a lokacin.

A cewar sabuwar dokar, akwai yuwuwar a shirya gudanar da zabuka kafin karewar lokacin wa’adin mulkin rikon, idan yanayin tsaro ya bada dama.

Dokar ta kuma bai wa Ibrahim Traore, shugaban mulkin soja na kasar, damar tsayawa takarar shugabancin kasar a lokacin gudanar da zabuka. (Fa’iza Mustapha)