Xi Jinping ya amsa sakon dalibai masu koyon harshen Sinanci dake kasar Hadaddiyar Daular Larabawa
2024-05-26 19:10:33 CMG Hausa
Kwanan nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya amsa sakon wakilan dalibai masu koyon harshen Sinanci dake makarantu daban-daban na Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ya karfafa musu gwiwar ci gaba da karatun Sinanci da kara fahimtar kasar Sin, don bayar da gudummawarsu ga karfafa dankon zumunta tsakanin kasashen biyu.
A watan Yulin shekara ta 2019, a gaban shugaba Xi gami da yariman Abu Dhabi dake Hadaddiyar Daular Larabawan na wancan lokaci, wanda shi ne shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa na yanzu, Mohammedbin Zayed al-Nahyan, kasashen biyu suka rattaba hannu kan wata takardar bayani, inda suka kaddamar da “aikin dake kunshe da makarantu 100” masu koyar da harshen Sinanci a Hadaddiyar Daular Larabawan. Kawo yanzu, akwai makarantun kasar 171 da suke koyar da harshen Sinanci, kana kuma adadin daliban dake karatun harshen ya kai dubu 71.
Kwanan nan ne, wakilai 40 na daliban makarantun Hamdan da Yas dake Hadaddiyar Daular Larabawa, suka aike da sako zuwa ga shugaba Xi Jinping cikin harshen Sinanci, inda suka bayyana kaunarsu ga al’adun kasar Sin, da burinsu na zama gadar sada zumunta tsakanin kasashen biyu. (Murtala Zhang)