logo

HAUSA

Xi zai halarci bikin bude taron ministoci karo na 10 na dandalin hadin kan kasashen Sin da Larabawa

2024-05-26 17:22:54 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, zai halarci bikin bude taron ministoci karo na 10 na dandalin tattauna hadin kan Sin da kasashen Larabawa da za a yi a ranar 30 ga watan Mayu, a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Hua Chunying ce ta sanar da hakan a yau Lahadi, inda ta ce shugaba Xi Jinping zai kuma gabatar da jawabi yayin bikin. (Fa’iza Mustapha)