Hukumar IOM ta yi hasashen bala’in zaizayar kasa da zabtarewar laka a Papua New Guinea ya yi ajalin mutane sama da 670
2024-05-26 20:25:59 CMG Hausa
Rahotanni sun ruwaito cewa, bisa hasashen da hukumar kula da masu kaura ta duniya ta Majalisar Dinkin Duniya wato IOM ta yi, adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon mummunan bala’in zaizayar kasa da zabtarewar laka a kasar Papua New Guinea ya zarce 670.
Iftila’in zaizayar kasa da zabtarewar laka ya afkawa wani kauye dake lardin Enga na kasar Papua New Guinea a ranar 24 ga wata, kuma ya zuwa ranar 26 ga wata, wato sa’o’i 48 ke nan bayan faruwar bala’in, gwamnatin kasar ba ta fayyace adadin mutanen da suka rasa rayukansu ko ji rauni ba. (Murtala Zhang)