logo

HAUSA

Firaministan Sin ya sauka a Seoul domin halartar taron kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu

2024-05-26 21:40:49 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya isa binin Seoul a yau Lahadi, domin halartar taron kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu da aka fara daga yau Lahadi zuwa gobe Litinin.

Za a yi taron ne bayan sama da shekaru 4 da dakatar da shi a shekarar 2019.

A yau Lahadi, bisa agogon wurin, Li Qiang ya gana da shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol da Firaministan Japan Fumio Kishida bi da bi, a birnin Seoul. (Fa’iza Mustapha)