Shugaban kasar Nijar ya tattauna tare da sarakunan gargajiya na kasar
2024-05-26 17:02:13 CMG Hausa
Shugaban kwamitin ceton kasa CNSP, kuma shugaban kasar Nijar, birgadiye janar Abdourahamane Tiani ya tattauna a ranar jiya Asabar 25 ga watan Mayun shekarar 2024, tare da tawagar sarakunan gargajiya na kasar Nijar.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Ita dai wannan ganawa na cikin tsarin tattaunawa tare da bangarori daban daban da shugaban Nijar ya kaddamar tare da wakilan al’umma da zummar sauraren muhimman bukatun ‘yan kasar Nijar.
A karshen wannan ganawa, sarkin Mirriah, kuma shugaban kungiyar sarakunan gargajiya, mai martaba Moutari Moussa, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya sun tattauna sosai tare da shugaban kasa kan batutuwan da ke ci ma ‘yan kasa tuwo a kwarya da suka hada da tattalin arziki, zaman lafiya, rayuwar al’umma da tsaro.
Shugaban kasa ya nuna farin cikinsa game da gudunmuwar da sarakunan gargajiya suke bada wa wajen kiyaye ‘yancin kasa da tabbatar da zaman lafiya da zaman jituwa tsakanin al’ummomi, in ji mai martaba Moutari Moussa.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.