logo

HAUSA

An bayyana karancin ilimi a matsayin babbar matsalar tabarbarewar harkokin tsaro a Arewacin Najeriya

2024-05-26 17:00:15 CMG Hausa

Gwamnan jihar Katsina Dr Umar Dikko Radda ya ce wajibi ne sai gwamnati ta bayar da kulawa a muhimman bangarorin kyautata rayuwar jama`a muddin tana son maganin rashin tsaron da yanzu haka ya addabi shiyyar arewacin Najeriya.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma`a 24 ga wata a garin Gusau fadar gwamnatin jihar Zamfara yayin taron lacca kan bikin yaye daliban jami`ar gwamnatin tarayyar dake Gusau, ya ce rashin tsaro da zaman lafiya suna mutukar shafar bangaren ilimi a kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Gwamnan na jihar Katsina ya bayyana takaicin ganin yadda yanzu haka Najeriya ke kan mataki na 144 a kididdigar zaman lafiya na duniya, lamarin da ya danganta da rikice-rikicen cikin gida.

Ya ce mummunan ayyukan `yan ta`adda musamman masu garkuwa da mutane a jahohin Katsina da Zamfara da Sokoto da Kaduna ya haifar da koma baya sosai ga harkar karatun yara, domin a yanzu haka kaso 10 na makarantun da suke a jihar Katsina suna a rufe saboda rashin tsaro.

A don haka gwamnan na jihar Katsina ya ce sai lallai gwamnatoci a dukkan matakai sun toshe kofofin da suke baiwa matasa da sauran jama`a damar shiga ayyukan ta`addanci ko taimakawa `yan ta`adda, sannan a samu saukin al`amura.

Bayan haka kuma gwamnan na jihar Katsina ya sake   kawo shawarar cewa yana da kyau kuma gwamnati ta karfafa tsarin tattara bayanan sirri, da kyautata tsarin kai dauki cikin hanzari kana da shigo da al`umma wajen aikin dakile karuwar matsalolin tsaro.

“Kara inganta tsarin ayyukan jami`an tsaron sa kai na gida zai yi mutukar taimakawa wajen kyautata harkokin tsaro a makarantu tare da kare duk wata barazana da za a iya kaiwa bangaren ilimi.”

“Babu kasar da zata cigaba ba tare da mafi yawan al`ummar ta suna da ilimi ba”(Garba Abdullahi Bagwai)