logo

HAUSA

An fara aikin gina yankin masana’antun jigilar hajoji dake tashar Lekki ta Najeriya

2024-05-26 16:34:49 CMG Hausa

Tashar Lekki dake birnin Ikkon tarayyar Najeriya, tashar jiragen ruwa ce mai zurfi ta farko ta zamani a kasar. Tun da aka fara aiki da ita a watan Janairun shekara ta 2023, kawo yanzu, adadin hajojin da ake jigilarsu ta tashar Lekki na dada karuwa. Kuma a ranar 24 ga watan Mayun bana, an kaddamar da aikin gina wani yankin masana’antu mai aikin jigilar hajoji a tashar Lekki, da nufin kyautata hidimomin tashar, gami da inganta ayyukan karbar kayayyaki yadda ya kamata.

Rahotannin sun ruwaito cewa, fadin yankin masana’antun jigilar hajoji dake tashar Lekki, ya kai kadada 40, fadin da ya yi daidai da na yankin tashar jiragen ruwan Lekki, wanda za’a kammala aikin ginawa nan da shekaru biyu masu zuwa. An ce, za’a iya gudanar da ayyuka daban-daban a yankin, ciki har da ajiyewa gami da raba wasu manyan hajoji, kamar albarkatun ma’adinai, da amfanin gona da sauransu, da samar da hidimomin karbar kayayyaki ba tare da bata lokaci ba, kaza lika, ayarin motocin dake akwai a yankin, zai iya biyan bukatun ayyukan jigilar hajoji iri-iri, cikin sauki da tsaro, a duk fadin Najeriya.

Makasudin gina yankin masana’antun jigilar hajoji dake tashar Lekki shi ne, domin kara biyan bukatun dake akwai, na yin shige da ficen kayayyaki tsakanin kasar Sin da kasashen yammacin Afirka, da ciyar da hidimomin jigilar hajoji gaba a tashoshin jiragen ruwan Najeriya. (Murtala Zhang)