logo

HAUSA

An kawo karshen taron `yan majalissar Ecowas a Najeriya tare da zabar mace a karon farko a matsayin kakakin majalissar

2024-05-25 14:42:11 CMG Hausa

Majalissa ta 6 ta kungiyar `yan majalissun kungiyar Ecowas ta zabi Madam Memounatou Ibrahim a matsayin kakaki a karshen taron musamman da kungiyar ta gudanar ranar alhamis 23 ga wata a birnin Kano dake arewacin Najeriya.

Wannan dai shi ne karo na faro a tarihin majalissar da ta zabi mace a kan wannan mukami, an kuma zabe ta ne tare da sauran shugabanni da za su taimaka mata wajen tafiyar da harkokin majalissar har zuwa nan da shekaru 4 masu zuwa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Madam Memounatou Ibrahima `yar kasar Togo itace ta gaji  Rt.Hon Sidie Mohamed Tunis wakili a majalissar dokokin kasar Sierra Leone wanda ya jagoranci majalissa ta 5 da ta shude.

A jawabin ta na farko bayan nadin nata, Madam Memounatou Ibrahim ta bayyana godiyar ta ga `yan majalissar bisa amincewar da suka yi mata wajen dora ta kan wannan mukami, wannan kamar yadda ta ce ya nuna a fili irin yadda kungiyar Ecowas ke mutuntawa tare da kare martabar mata da matasa.

Haka zalika sabuwar kakakin majalissar kungiyar Ecowas ta yabawa shugabannin Najeriya da Togo bisa yadda gwamnatocin su ke bayar da goyon baya ga ci gaban mata da matasa, inda ta ba da misali da yadda yanzu haka kasar Togo ta samar da wata doka da za ta taimakawa matasa da matan dake kasar.

“Yan majalissar kasashen da suke cikin kungiyar Ecowas yau sun zabe mu, mu zama shugaban wannan majalissa Ecowas Parliament muna murna, muna murna kuma mun zo kasar Kano” 

Ta sha alwashin cewa za ta yi bakin kokarin ta wajen ganin ta tabbatar da kyakkyawan zaton da kasashe membobin kungiyar ke yi mata.

Tace yanzu sake dawowar ayyukan ta`addanci da juyin mulki a janhurriyar Nijar da Burkina Faso da Mali da kuma matsalar sauyin yanayi sune manyan matsalolin dake damun shiyyar yammacin Afrika, kuma ta tabbatar dacewa majalissar za ta hada kai da membobin kasashe wajen maganin matsalolin wadanda dama dai suna cikin muradun da majalissa ke son cimmawa nan da 2050.

Daga karshe ta jinjinawa mataimakin shugaban majalissar dattawan Najeriya Sanata Barau Jibril kuma mataimakin kakakin majalissar ta Ecowas bisa amfani da kwarewar sa ta shugabanci wanda ya kai ga daukaka matsayin majalissar kungiyar ta Ecowas a yanzu.(Garba Abdullahi Bagwai)