logo

HAUSA

Ministan kudin Zimbabwe ya jinjinawa gudummawar masu zuba jari daga Sin

2024-05-25 16:01:21 CMG Hausa

Ministan ma’aikatar kudi na kasar Zimbabwe Mthuli Ncube, ya jinjinawa gudummawar da masu zuba jari daga kasar Sin ke bayarwa, ga ci gaban kasar dake kudancin nahiyar Afirka.

Ncube, wanda ya bayyana hakan a jiya Juma’a ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, yayin wata tattaunawa a gefen taron masu ruwa da tsakani a fannin masana’antun Zimbabwe, a birnin Harare fadar mulkin kasar, ya ce cikin shekaru kusan 20, adadin Sinawa masu zuba jari a kasar ya yi ta karuwa, lokacin da kasar ta yi fama da takunkuman kasashen yamma, wanda hakan ya sa sassa da a baya suka kyamaci kasar, a yanzu ke sake nazarin damammakin zuba jari a kasar.

Ministan ya kara da cewa, Sin ta zamo ginshiki mai karfi na raya tattalin arzikin Zimbabwe a shekarun baya bayan nan, inda take samar da tallafin kudade, da lamuni domin bunkasa muhimman ayyuka a fannin samar da ababen more rayuwa. (Saminu Alhassan)