logo

HAUSA

Guterres: Hukuncin da Kotun Duniya ta yanke na hana daukar matakan soja a Gaza yana da karfin shari'a

2024-05-25 15:04:12 CMG Hausa

A jiya Juma'a, Kotun Duniya karkashin MDD ta yanke hukunci, bisa bukatar da kasar Afirka ta Kudu ta gabatar mata, na hana kasar Isra'ila daukar matakan soja a garin Rafah dake zirin Gaza. Inda kotun ta ce, Isra'ila ta kasa samar da shaidar nuna za ta iya tsare fararen hula, da rayuwarsu a Rafah, saboda haka kotun ta sanar da mataki na wucin gadi, inda aka bukaci Isra'ila da ta dakatar da matakin soja da take aiwatarwa a garin Rafah.

A dai jiyan, kakakin babban magatakardan MDD Stephane Dujarric ya sanar da cewa, mista Guterres ya riga ya lura da matakin wucin gadin da Kotun Duniyar ta gabatar, ya kuma ce duk wani hukuncin da kotun ta yanke yana da karfi na shari'a, bisa kundin dokar Kotun Duniya.

A nata bangare, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu wadda ta gabatar da karar ga Kotun Duniya, don neman haramta matakan soja da kasar Isra'ila ke dauka a Rafah, ta ce tana farin ciki da hukuncin da Kotun Duniyar ta yanke, ta kuma kalubalanci Isra'ila da ta bi umarnin kotun. (Bello Wang)