logo

HAUSA

Fu Cong: Tsarin gudanar da harkokin duniya na bukatar kwaskwarima da kyautatuwa

2024-05-24 14:34:38 CMG Hausa

 

Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong, ya yi jawabi a muhawarar inganta karfin kasashen Afrika wajen tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta a fannin tsaro da ci gaba, inda ya bayyana wajibcin daidaita rashin adalcin da aka nuna wa kasashen Afrika a tarihi, da gaggauta kyautata tsarin gudanar da harkokin duniya.

A cewarsa, tsarin na bukatar kwaskwarima da kyautatuwa, da shawo kan matsalolin da aka samu sakamakon rashin adalci a fannin hakkoki da zarafi da ka’idoji. Ya ce Sin na maraba da AU da sauran kasashen Afrika, su shiga cikin kungiyoyin G20 da BRICS, da inganta hadin kanta da kasashen a karkashin inunwar tsarin BRICS+ da dai sauransu, a kokarin samar da dandali mai yakini ga Afrika, wajen shiga harkokin duniya. Haka kuma, Sin na goyon bayan daukar matakan a zo a gani, wajen baiwa kasashen Afrika damar fadin albarkacin bakinsu da kyautata matsayinsu na wakilci a cikin tsare-tsare da hada-hadar kudade na duniya.

Game da batun yi wa kwamitin sulhu na MDD kwaskwarima, ya ce Sin na da ra’ayin daukar mataki na musamman don biyan bukatun kasashen Afrika, a kokarin daidaita rashin adalcin da aka nuna masu a tarihi.

Fu Cong ya kara da cewa, a ko da yaushe, Sin na sanya batun inganta hadin kai da Afrika a gaban komai, ta fuskar diplomasiyya. Kazalika, za ta kira sabon taron koli na dandalin tattauna hadin kan Sin da Afirka na FOCAC a lokacin kaka na bana. Ya ce ta hanyar taron, Sin na fatan inganta dangantakar hadin kai da abota a tsakanin bangarorin biyu zuwa sabon matsayi, ta yadda za ta taka rawar gani wajen tabbatar da samun zaman lafiya da bunkasuwa mai karko a Afrika cikin dogon lokaci. (Amina Xu)