Sin da Brazil sun cimma matsayi daya kan warware matsalar Ukraine ta hanyar siyasa
2024-05-24 14:38:25 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da mashawarcin shugaban kasar Brazil Celso Amorim jiya Alhamis a birnin Bejing, fadar mulkin kasar Sin. Inda suka yi musayar ra’ayoyi kan yadda za a dauki matakan siyasa domin warware matsalar Ukraine, tare da yin kira da a sassauta yanayin yankin. Sun kuma cimma matsayi daya kan batun a fannoni shida.
Na farko shi ne, a yi kira ga bangarorin da abin ya shafa da su bi ka’idoji uku domin sassauta yanayin yankin, wato kada a habaka yakin zuwa sauran wurare, kada a dauki karin matakan tsananta yanayin yakin, kuma kada bangarori masu ruwa da tsaki su rura wutar yake-yake.
Na biyu shi ne, suna ganin cewa, shawarwari shi ne kadai hanyar da ta dace na warware rikicin kasar Ukraine.
Na uku shi ne, a kara samar da taimakon jin kai ga wuraren da rikicin ya shafa, domin kandagarkin karuwar barazanar jin kai.
Na hudu shi ne, a yi adawa da amfani da makaman kare-dangi, musamman ma makaman nukiliya da makamai masu guba.
Na biyar, a yi adawa da kai hare-hare ga tashoshin nukiliya na samar da wutar lantarki, da ma sauran na’urorin nukiliya da ake amfani da su cikin lumana.
Na shida kuwa shi ne, adawa ga masu hana mu’amala tsakanin kasa da kasa, don kafa kungiyoyin siyasa da na tattalin arziki da ba sa mu’amala da sauran bangarori.
Kana kasashen Sin da Brazil sun yi kira da a karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen duniya a fannin kare tsaron amfani da makamashi, da kudade, da cinikayya, da wadatar hatsi, tare da kiyaye tsaron ababen more rayuwa masu muhimmanci, kamar bututun sufurin iskar gas da man fetur, da wayoyin da aka shimfida a karkashin teku, da na’urorin samar da wutar lantarki, da wayoyin aika sako ta haske da dai sauran makamantansu, ta yadda za a kiyaye tsarin samar da kayayyaki tsakanin kasashen duniya yadda ya kamata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)