logo

HAUSA

Rundunar sojojin kasar Sin ta ci gaba da yin atisayen soja a wuraren dake kewayen tsibirin Taiwan

2024-05-24 11:17:06 CMG Hausa

Mai magana da yawun rundunar sojan ‘yantar da jama’ar kasar Sin reshen gabashin kasar, babban kanar na runudnar sojin ruwan kasar,  Li Xi, ya bayyana cewa, yau Juma’a, 24 ga wata, rundunar sojojin ta ci gaba da yin atisayen soja mai lakabin “Joint Sword-2024A” a yankunan teku dake kewayen tsibirin Taiwan, a kokarinta gwada karfin sojan na kwace ikon mallakar sararin samaniya da teku da sadarwa da karfin kai hare-hare cikin hadin kai, da kuma karfin mamaye muhimman yankuna. (Amina Xu)