logo

HAUSA

Sabon shugaban kasar Chadi ya yi rantsuwar kama aiki

2024-05-24 09:52:39 CMG Hausa

 

Mahamat Idriss Deby ya yi rantsuwar kama mulkin shugabancin  jamhuriyyar Chadi, jiya Alhamis a N'Djamena, fadar mulkin kasar, yayin wani biki da ya samu halartar shugabanni da manyan jami’ai daga wasu kasashe.

A yayin bikin, Mahamat Idriss Deby ya bayyana cewa, zai dukufa wajen yiwa kasarsa kwaskwarima a wa’adin aikinsa, a kokarin raya ingantaccen tattalin arziki da zamanintar da tsarin kiwon lafiya da ma gaggauta bunkasuwar sha’anin al’adu da yawon shakatawa.

Shekaru 5 ne tsawon wa’adin Mahamat Idriss Deby, kana zai iya neman ci gaban da rike mukamin sau daya. Shugaba Deby ya lashe zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 6 ga watan Mayu, da kashi 61 na kuri'un da aka kada.

A jiya da dare ne kuma gidan talibijin na kasar Chadi ya sanar da  umurnin Shugaba Deby na nada Allamaye Halina a matsayin sabon firaministan kasar. (Amina Xu)