logo

HAUSA

An binne marigayi shugaban kasar Iran Seyed Ebrahim Raisi

2024-05-24 10:55:06 CMG Hausa

An binne marigayi shugaban kasar Iran Seyed Ebrahim Raisi, jiya Alhamis a birnin Mashhad dake arewa maso gabashin kasar, wato garin da aka haife shi.

A wannan rana, an kai gawar marigayi shugaba Raisi zuwa filin jiragen sama na birnin Mashhad, sa’an nan, aka kai shi wuri mai tsarki na Imam Reza na birnin a cikin mota. Mutane da yawa sun taru a gefunan titunan da motar ta bi, don yin ban kwana da Shugaba Raisi. Wasu kuma suna dauke da hotonsa da kuma yin masa addu’a. Kana, akwai wasu mutane da suka yi ta ihun bayyana adawa da kasar Amurka da Isra’ila.

Kafar yada labarai ta kasar Iran ta IRNA ta ruwaito magajin birnin Mashhad Mohammad-Reza Qalandar Sharif na cewa, a kalla mutane miliyan 3 sun je yin ban kwana da marigayi Raisi.

A ranar 19 ga watan nan da muke ciki ne, jirgin sama mai saukar ungulu dauke da shugaban Iran Seyed Ebrahim Raisi da wasu manyan jami’ai, ya fadi a yankin duwatsu dake arewa maso yammacin kasar, hadarin da ya haddasa rasuwarsu. (Maryam)