logo

HAUSA

Ye Shiwen ta samu gurbi a gasar Olympic ta Paris

2024-05-23 13:40:24 CRI

‘Yar wasan linkaya ta kasar Sin, wadda ta yi nasarar lashe lambar zinari a gasar Olympic ta birnin London Ye Shiwen, ta samu gurbin shiga a fafata da ita, a gasar linkaya ta Olympic ta birnin Paris dake tafe, bayan da ta yi nasarar lashe linkayar mita 200 ajin mata, yayin gasar zakarun kasar Sin a tsakiyar makon jiya. Ye ta kai ga wannan nasara bayan jiran shekaru 8.

Yayin gasar ta zakarun kasar Sin, Ye ta kammala linkaya cikin mintuna 2:22.55, nasarar da ta haura wadda ta samu yayin gasar Olympic, inda a wancan karo ta gama linkaya cikin mintuna 2:23.91. A wannan karo ‘yar wasan linkaya Tang Qianting ce ta zo na biyu da lambar azurfa, yayin da  kuma Zhu Leiju ta zo na uku da lambar tagulla.

Game da hakan, Ye ta ce "Na yi matukar gamsuwa da wannan sakamako, wanda ya haura abun da na yi tsammani".

Kafin wannan lokaci, a baya ma Ye ta taba burge duniya, lokacin da ta lashe lambobin zinari biyu a gasar Olympic ta birnin London, lokacin tana da shekaru 16 a duniya. A shekarar 2017 ne kuma ta yi ritaya daga wasan linkaya, bayan ta gamu da rashin sa’a a gasar Olympic ta Rio, daga bisani kuma ta sake dawowa wasana a shekarar 2019. Ta sake yin rashin nasarar samun gurbin shiga gasar Olympic ta Tokyo, kana ta sake bayyana yin ritaya a karo na 2. Sai kuma a shekarar 2022 Ye ta sake bayyana dawowa wasan linkaya, tare da lashe lambar zinari a garin haihuwarta, wato birnin Hangzhou, wanda ya karbi bakuncin gasar wasannin nahiyar Asiya da ya gudana a shekarar.

Wannan karo, wato yayin gasar zakarun kasar Sin, ya kasance damarta ta karshe ta samun gurbin shiga gasar Olympic ta Paris, duba da shekarun ta 28 a yanzu, kuma wata kila ma damarta ta sake shiga wata gasar Olympic gaba daya.

Ye na matsayi na 11, kana ta yi rashin nasara a gasar linkaya ta mita 400, kwanaki 3 kafin yin sanarar mita 200, lamarin da ta ce ya tayar mata da hankali. Ta ce "Na fara tunanin barin gasar baki daya, bayan na yi rashin nasara a linkayar mita 400, amma goyon bayan masu sha’awar wasa na ya sa na ci gaba”. 

A gasar linkayar mita 200, ‘yar wasar da ta yi nasara a gasar Olympic Zhang Yufei ce ta lashe lambar zinari ajin mata, ta linkaya salon butterfly, cikin mintuna 2:06.40, kuma da hakan ta yi nasarar lashe lambobin zinari 3 a gasar. Sai kuma Chen Luying wadda ta zo ta biyu, yayin da Gong Zhenqi ta zo na 3.

Game da nasarar da ta samu, Zhang ta ce "Sakamakon ya yi kyau, amma ban gamsu da shi ba. Duk da hakan na yi iya kokari na".

A linkayar “backstroke” ajin maza kuwa, zakaran duniya Xu Jiayu, shi ne ya yi nasarar lashe mita 200, inda ya karbi lambar zinari bayan kammalawa a minti 1:57.70. sai kuma Wang Yutian da Tao Guannan dake biye da shi a matsayi na biyu da na uku. 

Tawagar tseren motoci ta McLaren na iya lashe gasar F1 nan zuwa shekarar 2025 in ji Piastri

 

Matukin motar tsere a tawagar kamfanin motar tsere ta McLaren, dake shiga babbar gasar Formula 1 Oscar Piastri, ya ce tawagarsa na iya karya matsayin bajimtar tawagar “Red Bull”, ta hanyar lashe babbar gasar tseren motoci ta “Grands Prix” kafin nan da shekarar 2025.

Tun bayan da mashirya gasar Formula 1, suka fara aiwatar da sabbin dokokin gudanar da gasar a shekarar 2022, tawagar “Red Bull” ce ke lashe dukkanin gasannin da ake fafatawa, inda tawagar ta lashe dukkanin kofunan gasar a manyan wasanni 42 cikin 49, ciki har da dukkanin wadanda aka gudanar a shekarar 2023 in ban da guda daya.

Bisa yanayin dokokin da ake da su a yanzu, wadanda za su wanzu ba sauyi har zuwa shekarar 2026, da yawa daga masu ruwa da tsaki a gasar F1, na ganin zai yi wuya sauran kungiyoyi su cimma nasarar doke tawagar “Red Bull” ya zuwa shekarar ta 2026.

Duk da haka, Piastri ya ce yana da kwarin gwiwar kaiwa ga saman dandamalin gasar nan zuwa shekara mai zuwa, duba da yadda suke kara matsawa kusa da makin da “Red Bull” ke samu a bana, sama da yadda suka kai a shekarar 2023.

Yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan nan, Piastri ya ce "A gani na za mu iya yin nasara kafin shekarar 2026. Duk da cewa “Red Bull” sun yi gaba da yawan lashe gasanni sama da sauran kungiyoyi, ina ga muna kara kusantarta. Idan muka dubi gasar Japan, a bara na kai ga nasarar samun matsayi na 2, rabin minti bayan dan kungiyar “Red Bull” wato Max, kana a bana ma ina baya da rabin minti inda na zo na 6, don haka dai ina ga kowa na kara matsawa gaba. Har yanzu, muna da sauran matakin da za mu taka tukuna, amma ina ga kowa na da kwarin gwiwar cewa za mu iya motsawa gaba har mu cimma nasara, mai yiwuwa a bana, kuma muna kara kaimin tunkarar kalubale a kakar wasa ta badi. Shekarar 2026 za ta zama sabon mafari ga kowa, amma akwai kyakkyawan fatan kungiyar McLaren za ta cimma nasarar lashe tseren da take shiga kafin sabbin dokokin gasar F1 su fara aiki".

Piastri, ya bayyana hakan ne gabanin bude babbar gasar tseren motoci ta cin kofin “Grand Prix” na kasar Sin, inda ya kammala a matsayi na 8, bayan ya fuskanci matsalar inji, amma abokin wasansa Lando Norris, ya ciwa tawagar McLaren matsayin direba mafi kwarewa na 2024, a matsayi na 2, inda ya raba makin tawagar “Red Bulls” wadda ta mamaye nasarar gasar.

Tawagar McLaren ta sha fama da kalubalen wasa a watanni 6 na shekarar bara, inda Norris da Piastri suka samu jimillar maki 29 kacal, a dukkanin wasannin manyan gasanni 9 da suka shiga a shekarar.

Sai dai kuma duk da hakan, tun daga tsakiyar kakar wasannin ta bara, tawagar McLaren ta amfani da motocin tsere kirar MCL60, sun sauya yanayin gasanni, inda tun daga zagaye na 10 zuwa sama, Norris da Piastri, suka hada jimillar maki 273, ciki har da kammala tsere kusa da layi a tsere 9, da yadda Piastri ya lashe tseren gajeren zango na Qatar.

Nasarar da tawagar McLaren ta samu ta ja hankalin masu sha’awar wasan tseren motoci, inda direban Alpine Esteban Ocon, ya shaidawa Xinhua cewa, bai taba ganin sauyin nasarar gasa a tsakiyar kakar wasa irin ta shekarar bara ba.

Da yake McLaren ta fara gasannin 2024 da kafar-dama, sama da kokarin da tawagar ta yi a 2023, Piastri na ganin tawagarsu za ta iya yin babbar bajimta nan gaba a bana, har su kai ga wuce sauran tawagogin karawar su.

Piastri ya ce "Tabbas wannan ne burin mu. Mun bude kakar bana cikin sa’a, sama da shekarar da ta gabata, kuma ina ganin muna da kwarin gwiwar nuna ci gaban wasan mu sama da yadda ta wakana a bara. A ganin mu, ba wani dalili da zai hana mu sake maimaita kwazon da muke yi. Muna cike da zumudin ganin mun cimma nasarar da tawagar mu za ta samu a kakar nan. Wasu kungiyoyin sun cimma nasarar dagawa zuwa mataki na gaba a lokacin hunturu zuwa yanzu. Ina ga matuka motar kamfanin Ferrari sun yi rawar gani tun fara kakar wannan shekara, amma ina fatan mu ma za mu yi kokari, mu kai ga wuce su, ina ga muna da kwarin gwiwar yin haka".