Firaministan Sin zai halarci taro na 9 na kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu
2024-05-23 20:14:10 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce firaministan Sin Li Qiang, zai halarci taro na 9, na kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu, wanda zai gudana a birnin Seoul, fadar mulkin koriya ta kudu.
Wang ya bayyana hakan ne a Alhamis din nan, inda ya ce taron kasashen uku zai gudana tsakanin ranaikun 26 zuwa 27 ga watan nan na Mayu. (Saminu Alhassan)