logo

HAUSA

An kaddamar taron tattaunawa game da raya al’adun Sin na 2024

2024-05-23 21:38:58 CMG Hausa

A yau Alhamis 23 ga wata ne aka gudanar da taron tattaunawa game da raya bangaren al’adu na kasar Sin na shekarar 2024 a birnin Shenzhen na lardin Guangdong.

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kuma shugaban sashen yada bayanai na kwamitin kolin JKS Li Shulei, ya halarci zaman tare da gabatar da jawabin kaddamarwa.

Taken taron na bana shi ne "Turbar kasar Sin ta zamanantarwa da sabon burin kasar na raya al’adu ", kuma sashen yada bayanai na kwamitin kolin JKS ne ya dauki nauyin shirya shi. (Saminu Alhassan)