Shugaban kasar Equatorial Guinea zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin
2024-05-23 19:04:50 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana a yau Alhamis cewa, shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, zai gudanar da ziyarar aiki a nan kasar Sin daga ran 26 zuwa 31 ga watan nan da muke ciki, bisa gayyatar takwaransa na kasar Sin Xi Jinping. (Amina Xu)