Ministan harkokin wajen kasar Masar ya isa kasar Iran don halartar taron jana’izar shugaban kasar Iran
2024-05-23 14:30:57 CMG Hausa
Jiya Laraba, ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar, ta ba da labari ta shafin kafar sada zumunta cewa, ministan harkokin wajen kasar Sameh Hassan Shoukry, ya isa birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, don halartar taron jana’izar shugaban kasar Iran marigayi Seyed Ebrahim Raisi, da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian, da dai sauran jami’an kasar da suka rasu, sakamakon hadarin jirgin sama mai saukar ungulu.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya bayar, an ce, wannan karon farko ne da Masar ta tura ministan harkokin waje zuwa Iran, tun bayan katse huldarta da kasar a shekarar 1980. Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta ce, kasar na tare da Iran a wannan lokaci na alhini.
Tun bayan da aka katse hulda tsakanin kasashen biyu, Masar da Iran sun kafa ofishin wakilci ne kawai a kasashen juna don kula da harkokin diplomasiyya. To sai dai kuma a baya bayan nan, huldarsu na kara kyautatuwa. A farkon wannan wata da muke ciki, yayin da aka gudanar da taron kolin kungiyar hadin kan Islama karo na 15, Sameh Hassan Shoukry na Masar, da Hossein Amir-Abdollahian na Iran, sun yi musanyar ra’ayi game da kyautata huldar kasashen biyu. (Amina Xu)