logo

HAUSA

Najeriya ta kafa alamu guda 1,200 akan iyakar ta da kasar Kamaru kamar yadda kotun kasa da kasa ta yi umarni

2024-05-23 09:36:25 CMG Hausa

Hukumar lura da shata kan iyakoki a tarayyar Najeriya ta ce ta samu nasarar kafa alamu guda 1,200 akan iyakar ta da kasar kamaru tun bayan hukuncin da kotun kasa da kasa ta yanke a kan yankin Bakkasi.

Shugaban hukumar Mr. Adamu Adaji ne ya tabbatar da hakan ranar 21 ga wata a birnin Abuja, lokacin da yake bayani kan nasarorin hukumar a wani bangare na shirye shiryen bikin cika shekara guda na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ce a shekarar da ta gabata hukumar ta samu karin kafa wasu alamu har guda dari biyar a kan iyakar da kasar Kamaru.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Ya ce hukumar ta dukufa wajen kafa alamun ne akan iyakokin ta da kasashe makwafta domin shawo kan matsalolin rikicin kan iyaka a tsakanin Najeriya da kasashen da take makwaftaka da su.

Mr.Adamu Adaji ya cigaba da cewa hakika wannan mataki da hukumar ta dauka ya haifar da nasarori sosai wajen aiwatar da hukuncin da kotun kasa da kasa ta yanke a tsakanin Najeriya da kasar Kamaru.

A bangaren iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar kuwa, shugaban hukumar yace duk da cewa akwai zaman lafiya a tsakani, amma hukumar tana kokarin hada kai da takwararta ta jamhuriyar Nijar domin kafa alamu akan iyakokin, ta yadda iyakokin kasashen biyu za su fito fili  sosai .

“Wannan iyaka tamu da jamhuriyar Nijar tana da tsawon kilomita 1,500, amma alamu 148 kawai aka samu kafawa tun lokacin mulkin mallaka, sai yanzu muka hada kai da takwarorin mu na jamhuriyar Nijar inda muka kara kafa alamu 200 a tsakanin tsoffin da ake da su”

Ta fuskar iyakar dake tsakanin jamhuriyar Benin da Najeriya kuwa ya ce ba a kai ga tantancewa ba, wannan tasa a shekarar bara hukumar ta fara zama da hukumomin kasar ta Benin domin fitar da iyakokin a zahiri.

Akan iyakokin dake tsakanin jahohi kuwa, shugaban hukumar ya ce a shekarar bara hukumar ta samu damar kafa alamun akan iyakokin dake tsakanin jahohi 15 dake tarayyar Najeriya, inda ya kara da cewa ko a makon jiya jami`an hukumar tasa sun ziyarci wasu al`ummomi a jihar Jigawa domin wayar masu da kai a game da shirin da ake yi na kara kafa alamu guda 40 a iyakokin dake jihar.(Garba Abdullahi Bagwai)