Shugaban Nijar ya jaddada amincewa da manufar kasar Sin daya tak a duniya
2024-05-23 19:24:10 CMG Hausa
A jiya Laraba 22 ga watan nan, jakadan kasar Sin a janhuriyar Nijar Jiang Feng, ya gana da shugaban gwamnatin sojin kasar Abdourahamane Tiani, da nufin yin musayar abota, game da bunkasa alakar Sin da janhuriyar Nijar, da karfafa hadin kai a fannin raya albarkatun mai.
Yayin zantawar ta su, Jiang Feng ya ce Sin da Nijar sun cimma nasarori da dama, na hadin gwiwa a fannin raya albarkatun mai. Ya ce kwanaki 3 kafin ganawar ta su, babbar kwantenar dakon mai ta farko, dauke da miliyoyin gangar danyen mai daga yankin hakar mai na Agadem, ta kama hanya a kan teku, wanda hakan ya shaida kasancewar Nijar daya daga cikin kasashe masu fitar da danyen mai a duniya.
A nasa bangare kuwa, shugaba Tiani, cewa ya yi Nijar na matukar nacewa, da goyon bayan manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya. Wanda hakan jigo ne da ba wani sashe da zai iya musantawa. (Saminu Alhassan)