logo

HAUSA

An fara atisayen soja na hadin gwiwa a kewayen tsibirin Taiwan

2024-05-23 10:02:32 CMG Hausa

Tun daga karfe 8 saura kwata na safiyar yau Alhamis, rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin reshen gabashin kasar, ta fara gudanar da atisayen soja na hadin gwiwa a mashigin tekun Taiwan, da yankunan arewaci, da kudanci, da gabashin tsibirin Taiwan, da kuma kewayen tsibiran Kinmen, da Matsu, da Wuqiu da kuma Dongyin.

Kakakin rundunar sojan, babban kanar Li Xi ya bayyana cewa, tun daga yau Alhamis har zuwa gobe Juma’a, rundunar sojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin reshen gabashin kasar ta shirya sojojin kasa, da na ruwa, da na sama, da rokoki da sauransu, don yin atisayen soja na hadin gwiwa, mai taken “Joint Sword-2024A”, a kewayen tsibirin Taiwan.

Jami’in ya ce hakan martani ne ga ayyukan ‘yan aware na yankin Taiwan, kuma kashedi ne da Sin ta aikewa kasashen waje, da suka tsoma baki cikin batun yankin Taiwan. (Zainab Zhang)