logo

HAUSA

Burtaniya za ta gudanar da babban zabe a ranar 4 ga watan Yuli

2024-05-23 13:47:21 CMG Hausa

Jiya Laraba, firaministan kasar Burtaniya Rishi Sunak ya sanar da cewa, za a gudanar da babban zabe a kasar a ranar 4 ga watan Yuli. Mista Sunak ya ce, ya zanta da sarki Charles III, inda ya gabatar masa da rokon kawo karshen wa’adin majalisar dokokin kasar, kuma sarki Charles ya amince da hakan.

Wata kuri’ar jin ra’ayin al’umma da aka kada ta nuna cewa, bayan Rishi Sunak ya kama aiki a matsayin firaministan kasar a watan Oktoban shekarar 2022, jam’iyyar adawa ta Labour Party, na samun karbuwa ga al’ummar kasar sama da jam’iyya mai mulki ta Conservative Party.

Kaza lika, sabbin bayanan da hukumar binciken ra’ayin al’umma ta YouGov ta kasar Burtaniya ta fidda, sun nuna cewa, ya zuwa ranar 16 ga watan nan da muke ciki, adadin masu goyon bayan jam’iyya mai mulki a kasar, ya kai kaso 20 bisa dari, yayin da adadin masu goyon bayan jam’iyyar adawa ya kai kaso 47 bisa dari. (Maryam)