logo

HAUSA

Mahara sun hallaka a kalla mutane 40 a wani kauye dake Jihar Plateau

2024-05-22 10:05:28 CMG Hausa

Wani jami’in jihar Plateau dake shiyyar tsakiyar tarayyar Nijeriya, ya bayyana a jiya Talata cewa, wasu mahara sun kai hari wani kauye dake jihar a daren ranar Litinin 20 ga watan nan, harin da ya haddasa rasuwar mutane a kalla 40.

Kwamishinan watsa labarai na jihar ta Plateau Musa Ibrahim Ashoms, ya bayyana cewa, a daren ranar Litinin, wasu mahara sun shiga kauyen Zurak, na yankin karamar hukumar Wase a kan babura, inda suka bude wuta tare da hallaka mutane a kalla 40.

Wasu kafofin watsa labarai na Nijeriya sun bayyana cewa, maharan sun bude wuta kan al’ummun kauyen, wanda hakan ya haddasa jikkatar mutane da yawa, tare da kone gidaje da dama. Kuma a halin yanzu, ana gudanar da binciken kan lamarin.   (Maryam)