Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga sabon shugaban kasar Vietnam
2024-05-22 19:05:50 CMG Hausa
A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sako ga sabon shugaban kasar Vietnam To Lam, inda ya yi masa fatan alheri sakamakon darewa shugabancin jamhuriyar gurguzu ta Vietnam.
A wani labarin kuma, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta sanar da cewa, wakilin musamman na shugaba Xi Jinping, kuma mataimakin firaministan majalisar gudanarwar kasar Zhang Guoqing, zai halarci taron jana’izar marigayi shugaban kasar Iran Seyed Ebrahim Raisi a birnin Tehran a yau Laraba.
A daga bangaren kuma, manzon musamman na shugaba Xi Jinping, kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin He Baoxiang, zai halarci bikin rantsar da shugaban kasar Comoros Azali Assoumani, wanda zai gudana a birnin Moroni, fadar mulkin kasar ta Comoros a ranar 26 ga watan nan na Mayu.(Safiyah Ma)