logo

HAUSA

Sin ta zama kasa mafi goyon baya da jagorantar harkokin kula da wanzuwar mabanbantan halittu a duniya

2024-05-22 20:23:22 CMG Hausa

A yau Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2019, Sin ta ci gaba da zama kasa da ta fi ba da tallafin kudi, ga yarjejeniyar wanzuwar mabanbantan halittu, da kuma babban kasafin kudinta. 

Wang ya ce Sin na nuna himma, da sauke nauyin dake wuyanta, tare da aiwatar da ayyuka masu amfani, ta kuma zamo kan gaba a goyon baya, da jagorantar harkokin kula, da wanzuwar mabanbantan halittu a duniya.

Game da hasashen da ake yi cewa, taron ministocin kudi na kungiyar G7 zai mai da hankali kan “Yadda Sin ta samar da kayayyaki fiye da kima”, Wang Wenbin ya bayyana cewa, zargin da Amurka ta yayata cewa wai “Sin na samar da kayayyaki fiye da yadda ake bukata a fannin masana’antun sabbin makamashi", ya kaucewa hakikanin gaskiya, da kuma dokokin tattalin arziki. Don haka ya yi fatan bangaren Turai zai cika alkawarinsa, na goyon bayan gudanar da harkokin kasuwanci cikin ‘yanci, da kuma adawa da ra’ayin ba da kariyar cinikayya.

Game da halin da ake ciki a tekun kudancin kasar Sin kuwa, Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Sin ta sake yin kira ga bangaren Philippines, da ya bi ka’idojin sanarwar ayyukan bangarori daban daban game da tekun kudancin kasar Sin.

Bugu da kari, game da yadda Amurka ta kakabawa wasu kamfanonin kasar Sin takunkumi ba tare da bin dokoki ba, bisa zargin “Yin cudanya da kasar Rasha”, a dai yau Laraba, ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana shirin aiwatar da martani, kan wasu masana'antun sojan Amurka, da manyan jami’ansu.(Safiyah Ma)