logo

HAUSA

Jami'ai sun yi kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka karkashin dandalin FOCAC

2024-05-22 19:32:25 CMG Hausa

Jami’an kasar Sin da na kasar Habasha, sun yi kira da a kara kyautata hadin gwiwa daga sassa mabanbanta tsakanin kasashen biyu, karkashin dandalin bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka ko FOCAC a takaici.

Jami’an sun yi kiran ne a jiya Talata, yayin taron manyan jami’ai mai lakabin "Waiwaye game da rawar da Habasha ke takawa a dandalin FOCAC, da kuma inda aka sanya gaba", wanda ya gudana a birnin Addis Ababa, fadar mulkin Habasha.

Da yake tsokaci yayin taron, shugaban ofishin ma’aikatar harkokin wajen kasar Habasha Eshete Tilahun, ya ce dandalin FOCAC ya zamo mai inganci, da karfin ingiza hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, ta hanyar bunkasa samar da ababen more rayuwa, da inganta hade sassa daban daban, da fadada hada hadar cinikayya, da jawo jarin waje na kai tsaye, da bunkasa sana’o’i a sassan nahiyar Afirka.

A nasa bangare kuwa, jami’in diflomasiyya a ofishin jakadancin Sin dake Habasha Yang Yihang, cewa ya yi dandalin FOCAC, ya samar da wani tsari na ingiza hadin gwiwar Sin da Afirka, zuwa matakin cimma manyan nasarori, matakin da ya sanya kasar Sin ta zama babbar abokiyar cinikayyar kasashen Afirka cikin shekaru 15 a jere. (Saminu Alhassan)