Sin ta nanata wajibcin kiyaye fararen hula ta hanyar kawo karshen rikici
2024-05-22 14:17:13 CMG Hausa
Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong, ya nanata wajibcin kawo karshen rikici don kiyaye fararen hula. Fu ya bayyana hakan ne cikin jawabinsa, yayin muhawarar kiyaye fararen hula a lokutan rikici, wadda kwamitin sulhu na MDD ya shirya a jiya Talata.
Fu Cong ya ce, rikicin dake addabar yankin Gaza a tsawo sama da watanni 7, ya haddasa rasuwa, da jikkatar fararen hula, da matsalar jin kai da ba a taba ganin irinsu ba. Kuma a halin yanzu, miliyoyin fararen hula da suka shiga Rafah don neman mafaka suna cikin halin bukatun gaggawa. Ya ce ya kamata kwamitin sulhun ya gaggauta mai da batun tsagaita bude wuta gaban komai, ya kuma dauki matakin da ya wajaba don kalubalantar Isra’ila, da ta dakatar da kai hari kan fararen hula Palasdinawa, ta daina gudanar da ayyukan soja a Rafah, don baiwa fararen hula kyakkyawan fatan rayuwa.
Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, ta bayyana a jiya Talata cewa, ya zuwa yanzu, an katse hanyar shigar da tallafin gaggawa na jin kai a fannin kiwon lafiya zuwa yankin Gaza daga Masar, yayin da sassan kasa da kasa ke yin kira ga Isra’ila, da ta kawar da shingayen da ta kafa a zirin Gaza, ta amince da shigar kayayyakin tallafi zirin, don sassauta matsalar jin kai da ake fuskanta.
A jiya Talata, kamfanin dillancin labarai na Palasdinu, ya ce sojojin Isra’ila sun kai hari ta sama, a wasu yankuna dake arewaci da kudancin yankin Gaza, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane a kalla 19. (Amina Xu)