Wang Yi ya halarci taron kwamitin ministocin harkokin wajen kasashe mambobin SCO
2024-05-22 14:13:33 CMG Hausa
A jiya Talata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya halarci taron kwamitin ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO, a birnin Astana fadar mulkin kasar Kazakhstan.
A yayin taron, Wang Yi ya nuna cewa, a halin yanzu duniya na samun saurin sauye-sauye, tare da ci gaba, da fama da tangarda. Ya ce wasu kasashe na aiwatar da matakan babakere, da kafa karamar gamayya, da zartas da manufofin kashin kansu, don matsa lamba, da tsoma baki cikin harkokin sauran kasashe, kana suna yunkurin katse hulda da wasu, ta yadda suke karawa ‘yan aware, da ‘yan ta’adda, da masu tsattsauran ra’ayi kwarin gwiwa, da zummar matsa lamba kan kasashe masu tasowa dake dogara da karfin kansu, da toshe hanyar farfado da kasuwanni masu saurin ci gaba, da karfi, da kuma kasashe masu tasowa.
Wang Yi ya ce “Dole ne mu nace ga ruhin Shanghai, wato amincewa juna, da cimma moriyar juna, da zaman daidaito da gudanar da shawarwari, da mutunta mabambantan al’adu, a kokarin samun ci gaba tare. Duk da karin sauye-sauye da duniya ke fuskanta, ya dace mu bi hanyar da ta dace, mu inganta karfin kungiyar ta SCO, don kiyaye muradu na bai daya, da tinkarar kalubaloli cikin hadin kai, da kare adalci da daidaito.
Wang Yi, ya kuma ba da shawarwari guda hudu. Da farko, a nacewa dogaro da kai bisa manyan tsare-tsare da yin hadin gwiwa. Na biyu kuwa, a daidaita kalubaloli, da wahalhalu cikin hadin kai, da daga matsayin hadin gwiwa. Na uku kuma, a tsaya tsayin daka wajen cimma moriya tare bisa hadin kai. Na karshe, a yi hakuri da juna, da zurfafa mu’ammala da koyi da juna. (Amina Xu)