Iran: Za a yi bincike game da hadarin jirgin da ya yi hadari dauke da shugaban kasar
2024-05-21 11:27:00 CMG Hausa
Kamfanin dillancin labarai na kasar Iran, ya labarta a jiya Litinin cewa, babban hafsan sojojin kasar Mohammad Hossein Bagheri, ya umurci wata tawaga ta musamman, da ta nazarci musabbabin faduwar jirgin sama mai saukar ungulu, dake dauke da shugaba Seyed Ebrahim Raisi da sauran jami’an kasar da suka rasu sakamakon hadarin. An ce, tuni wannan tawaga ta isa wurin da hadarin ya auku, kuma za ta gabatar da sakamakon bincikenta bayan kammala aikin.
A dai jiyan, kwamitin tabbatar da kundin tsarin mulkin kasar Iran ya sanar da cewa, mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad Mokhber yana tafiyar da harkokin shugaban kasa, ya zuwa lokacin gudanar da babban zaben shugaban kasar da za a yi nan da kwanaki 50.
Jim kadan da jin labarin rasuwar shugaban Iran Raisi, shugabanni da gwamnatocin kasa da kasa sun rika bayyana ta’aziyyarsu, ciki har da shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ya mika sakon alhini ga mataimakin shugaban kasar Mohammad Mokhber a jiya Litinin, don jajantawa iyalan Raisi da al’ummar Iran.
Shi ma shugaban tarayyar Najeriya Bola Tinubu, a madadin gwamnati da al’ummar kasarsa, ya gabatar da ta’aziyyar rasuwar shugaba Raisi.
Kaza lika, shugabannin kasashen Rasha, da Turkiya, da Masar, da hadaddiyar tarayyar Larabawa, da Jordan, da Sham, da Qatar, da Pakistan, da Venezuela, da Indiya, da babban sakataren kungiyar tarayyar Larabawa Ahmed Aboul Gheit, da shugaban kwamitin Turai Charles Michel, su ma sun gabatar da ta’aziyyarsu.
A ranar Lahadi ne dai jirgin sama mai saukar ungulu dauke da shugaban Iran Seyed Ebrahim Raisi, da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian, da wasu jami’an kasar, ya gamu da hadari, inda ya fadi a lardin gabashin Azarbaijan dake arewa maso yammacin kasar, hadarin da ya haddasa rasuwarsu. (Amina Xu)