logo

HAUSA

Xi ya taya zababben shugaban Chadi Mahamat Deby murna

2024-05-21 18:47:40 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya taya Mahamat Idris Deby Itno, murnar lashe zaben shugaban kasar jamhuriyar Chadi.

Xi Jinping ya ce a shekarun baya-bayan nan, dangantakar Sin da Chadi ta ci gaba da habaka, kana aminci a tsakaninsu ya kara zurfi, kuma hadin gwiwarsu a fannoni daban-daban na ta samun ci gaba, baya ga kara hadin kai da suke yi kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa.

Ya ce yana daukar batun raya dangantakar Sin da Chadi da muhimmanci, kuma a shirye yake ya hada hannu da shugaba Mahamat Deby, wajen karfafa goyon bayan juna da inganta hadin gwiwar abota a tsakaninsu, ta yadda al’ummominsu za su kara cin gajiyarsa. (Fa’iza Mustapha)