Wang Yi: Sin za ta ci gaba da aiki tare da Rasha wajen kare tsaro da daidaito a shiyyarsu
2024-05-21 11:59:29 CMG Hausa
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce Sin ta shirya yin hadin gwiwa da kasar Rasha, da ma sauran kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai ko SCO, ta yadda za su bunkasa tsaro da daidaito, da ci gaban shiyyarsu, da ingiza kyakkyawan jagorancin duniya, wanda zai haifar da adalci da dora duniya kan turba ta gari.
Wang, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya yi wannan tsokaci ne yayin ganawarsa da takwaransa na Rasha Sergey Lavrov, a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar SCO, wanda ya gudana jiya Litinin a birnin Astana, fadar mulkin kasar Kazakhstan.
Kaza lika, yayin zantawar manyan jami’an biyu, Wang ya jinjinawa matsayar shugaba Putin na Rasha, game da batun yankin Taiwan, yana mai cewa, ya yi imani Rasha za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan dukkanin batutuwan da suka shafi moriyar kasar Sin.
Ya ce, a halin da ake ciki, burin samar da SCO mai hadin kai da cimma moriyar juna, ya yi daidai da muradun daukacin kasashe mambobin kungiyar, baya ga kasancewar hakan wata dama ta tabbatar da tasirin mabambantan sassa a duniya.
A nasa bangare kuwa, mista Lavrov cewa ya yi, Rasha a shirye take ta yi aiki tare da kasar Sin, wajen wanzar da musaya a dukkanin fannoni, da ingiza hadin gwiwa a dukkanin sassa. Game da batun Taiwan kuwa, Lavrov ya ce, Rasha ta fayyace matsayinta karara, kuma tana ci gaba da goyon bayan Sin, a fannin cimma nasarar dunkule dukkanin yankunan kasar. (Saminu Alhassan)