logo

HAUSA

Jagororin Afirka na Allah wadai da yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo

2024-05-21 11:05:38 CMG Hausa

 

Shugabannin kasashen Afirka, da hukumomi daban daban na ci gaba da yin Allah wadai da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da kungiyar raya yankin kudancin Afirka ta SADC, da Afirka ta Kudu, da Namibia na cikin sassan da tuni suka yi tir da yunkurin juyin mulkin na safiyar ranar Lahadi.

Da yake tsokaci game da hakan, shugaban hukumar gudanarwar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ya yi tir da amfani da karfin tuwo da nufin sauya ikon kundin tsarin mulki a duk wata kasa dake Afirka. Kaza lika Faki Mahamat, ya yi maraba da yadda jami’an tsaron Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo suka yi namijin kokarin shawo kan al’amarin.

Ita ma kungiyar SADC, wadda Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo daya ce daga mambobinta, ta taya Kinshasa murnar kawo karshen yanayin da ka iya tabarbarewa.

Rahotanni na nuna cewa, da misalin karfe 4:30 na asubahin ranar Lahadi, wasu dakaru kimanin 50 dauke da bindigogi, sun kutsa kai gidan dan takarar kujerar kakakin majalisar wakilan kasar Vital Kamerhe, inda suka yi musayar wuta da jami’an tsaro, kuma nan take wasu ‘yan sanda biyu da mahari daya suka rasu.

An ce, sauran maharan sun kutsa kai fadar gwamnatin kasar ta “Palais de la Nation”, inda ofishin shugaban kasar Felix Tshisekedi yake, kuma a nan ma an yi musayar wuta wadda ta kai ga cafke su.

Wani faifan bidiyo da ya rika kewayawa a shafukan sada zumunta na yanar gizo, ya nuna maharan sanye da kakin sojoji, suna daga tsohuwar tutar kasar ta Zaire, suna kuma ikiranin yunkurin sauya yadda al’amura ke gudana a kasar.    (Saminu Alhassan)