logo

HAUSA

Sin ta bayyana rashin jin dadi kan zargin da Amurka ta yi mata game da batun Ukraine

2024-05-21 16:12:02 CMG Hausa

 

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Geng Shuang, ya yi jawabi a jiya Litinin a gun taron binciken batun samarwa Ukraine makamai, wanda kwamitin sulhu na majalisar ya gudanar, inda ya nuna matukar rashin jin dadi game da zargi maras tushe da wakilin kasar Amurka ya yi wa kasar Sin.

A cewarsa, da farko, Sin ba wadda ta haifar da rikicin Ukraine ba ce, kuma ba ta da alaka da wannan matsala, kana ba ta samarwa bangarorin da rikicin ya shafa ko wadanne nau’i na makamai ba.

Kazalika, Sin ba za ta dauki mataki irin na Amuka ba, wadda ta tsawaita lokacin rikicin, don ta ci moriya daga hakan. Sin na tsayawa tsayin daka kan gaggauta yin shawarwari, da daidaita matsalar a siyasance. Na biyu, Sin na da ‘yancin yin cinikayya da kasashen duniya ba tare da ko wane shinge ba ciki har da Rasha, kuma babu wani dalili da zai kawo cikas ga cinikayyarta. Sin tana kayyade sayar da hajojin da ke da amfani a zaman rayuwar yau da kullum da kuma ayyukan soja zuwa sauran kasashe.

Don haka kasar Sin na kalubalantar Amurka, da ta dakatar da shafawa kasar Sin bakin fenti, da daina kakabawa kamfanonin Sin takunkumai na kashin kai ba tare da dalili ba. Na uku, al’ummar duniya na da masaniya a fili game da manufofi da matakan da Amurka ke dauka kan batun Ukraine, kuma Sin din na shawartar Amurka da ta yi dogon tunani, ta dakatar da dora laifi kan sauran sassa, kana ta bi hanyar da ta dace wajen warware rikicin Ukraine. (Amina Xu)