logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Kano tace za ta goyi bayan duk hukuncin da aka zartar kan mutumin da ya yi sanadin mutuwar mutane 17 a masallaci

2024-05-21 14:01:19 CMG Hausa

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf yace zai goyi bayan duk hukuncin da kotu ta zartar kan mutumin da ake tuhuma da fashewar wani abu a masallaci a dai dai lokacin da mutane ke gudanar da ibada a kauyen Gadan dake yakin karamar hukumar Gezawa.

Gwamna ya tabbatar da hakan ne jiya Litinin 20 ga wata, lokacin da ya kai ziyarar jaje ga iyalai da `yan uwan mutanen da suka jikkata da kuma wadanda suka rasa rayukansu sakamakon faruwar al`amarin.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya kadu sosai bayan da shugabannin hukumomin tsaro dake jihar suka sanar da shi abun da ya faru, lokacin yana birnin Abuja wajen wani taro da wakilan majalissar dinkin duniya.

Ya ce a lokacin da aka sanar da shi babu mutum guda da ya rasu, amma ya zuwa jiya Litinin an ba shi labarin mutuwar mutane 17 daga cikin 25 da hatsarin ya ritsa da su, wanda 8 daga cikin su suke karbar magani a asibiti.

Gwamnan na jihar Kano ya shaida cewa kafin ya kawo ziyara kauyen, sai da ya biya ta asibitin Murtala inda aka kwantar da mutane, inda ya jajanta tare da ba su tallafin kudi har dubu 100 kowannen su sannan kuma gwamnati za ta cigaba da lura da lafiyar su har lokacin da za su samu sauki.

“Gwamnati ta kafa kwamiti na musamman, sai an yi bincike mai karfi akan musabbabin faruwar al`amari, shi kan sa wanda ya aikata wannan mugun aiki sai mun bincike shi, in dai ka aikata laifi bisa ganganci da rashin imani, to babu shakka gwamnati ba za ta kyale ka ba, a sabo da haka muna tabbatar muku musamman ku iyalan wadannan mamata cewa idan jami`an tsaro sun gama bincike, za a kai shi kotun shari`ar musulunci, saboda haka muna kiran ku da ku kwantar da hankulan ku”

Yanzu haka matashi da ya aikata wannan ta`addanci yana hannun jami`an tsaro inda ake shirye shiryen gurfanar da shi gaban kotu.(Garba Abdullahi Bagwai)