logo

HAUSA

Mai gabatar da kara a ICC ya bukaci a kama firaministan Isra’ila da wasu shugabannin Hamas

2024-05-21 10:04:38 CMG Hausa

 

Babban mai gabatar da kara a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC mista Karim Khan, ya ce ya gabatar da bukatar neman a kama wasu kusoshin gwamnatin Isra’ila su biyu, ciki har da firaministan kasar Benjamin Netanyahu, da wasu jagororin kungiyar Hamas su uku.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Karim Khan ya ce, akwai kwararan hujjoji dake nuna yadda Netanyahu da ministan tsaron Isra’ila Yoav Gallant, sun aikata laifukan yaki da muzgunawa bil Adama a zirin Gaza, tun daga ranar 8 ga watan Oktoban shekarar 2023.

Khan ya kara da cewa, manyan shugabannin Hamas 3 da yake zargi da aikata laifukan yaki a yankunan Isra’ila da zirin Gaza tun daga 7 ga watan Oktoban shekarar 2023, su ne Yahya Sinwar, da Mohammed Diab Ibrahim Al-Masri (Deif), da Ismail Haniyeh.   (Saminu Alhassan)