logo

HAUSA

Ma’aikatan kasar Sin sun taimaka ga inganta tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Kainji dake Najeriya

2024-05-21 17:41:54 CMG Hausa

A halin yanzu, tawagar dake aikin gine-gine da ta kunshi ma’aikata injiniyoyi, da na ma’aikatan fasaha kusan dari na Sin, suna aikin gina tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Kainji dake Najeriya, wadda ta kasance irinta mafi girma a kasar. Ma’aikatan kasar Sin na tsayawa tsayin daka a kan aikin su, suna kuma yin aiki tukuru, tare da nuna wa Afirka fasahohin ci gaban da kamfanonin kasar Sin ke da su, da irin jajircewar da ma’aikatan gine-ginen kasar ke yi. A cikin shirinmu na yau, bari mu je tashar samar da wutar lantarki bisa karfin ruwa ta Kainji, don ganin yadda ma’aikatan gine-gine na kasar Sin suka taimaka wajen ingantawa da fadada karfin tashar.