Sassa daban daban na mutunta “ka’idar Sin daya tak a duniya” da adawa da ballewar yankin Taiwan
2024-05-21 10:59:11 CMG Hausa
Kungiyoyin kasa da kasa da gwamnatocin kasashe da jam’iyyun daban daban, sun bayyana matsayinsu na nacewa ga “ka’idar nan ta kasar Sin daya tak a duniya”, da amincewarsu ga matsayin halastacciyar gwamnatin Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin daya tak a duniya, suna kuma adawa da ballewar yankin Taiwan daga kasar Sin, da ma sauran matakai na tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar. An bayyana hakan ne yayin da aka amsa tambayoyin ‘yan jarida, ko fitar da sanarwa da dai sauran hanyoyi.
Kwanan baya, hukumomin MDD, da sauran kungiyoyin kasa da kasa dake Geneva, sun nanata goyon bayansu ga kudurin babban taron majalisar mai lamba 2758, wanda ya bayyana nacewarsu ga “ka’idar kasar Sin daya tak a duniya”.
Cibiyar kasashe masu tasowa wato South Centre , ta nanata cewa, tana adawa da duk wani mataki na ballewar yankin Taiwan daga kasar Sin, tare da goyon bayan dunkulewar Sin cikin lumana.
Shi ma shugaban kwamitin nazarin huldar Najeriya da Sin na majalisar wakilan tarayyar Najeriya Ja’afaru Yakubu, ya yi nuni da cewa, Najeriya na kan “ka’idar kasar Sin daya tak a duniya” ba tare da tangarda ba, kuma yankin Taiwan wani bangare ne na kasar Sin da ba za a iya ware shi ba. A cewarsa, al’ummar Najeriya sun taba dandana wahalhalun yakin basasa, don haka abu ne mai sauki a iya fahimtar aniyyar al’ummar kasar Sin ta kare cikakkun yankunan kasa.
Kaza lika, kasashen Kongon Brazaville, da Botswana, da Lesotho, da Malawi, da Uganda da Afirka ta Kudu, da Habasha, da dai sauran kasashen duniya, suna nanata matsayinsu na nacewa ga wannan ka’idar. (Amina Xu)