Sama da wakilai 600 za su halarci taron kasashen Afirka karo na 9 game da yawan al’umma a Malawi
2024-05-20 10:58:32 CMG Hausa
Ministan ma’aikatar kudi da raya tattalin arziki a Malawi Simplex Chithyola Banda, ya ce sama da wakilai 600 za su halarci taron kasashen Afirka karo na 9 game da yawan al’umma, wanda zai gudana tun daga yau Litinin zuwa Juma’a 24 ga watan nan, a birnin Lilongwe fadar mulkin kasar.
Da yake yi wa manema labarai karin haske game da taron a ranar Asabar, mista Banda, ya ce taron zai hallara baki daga sassan nahiyar Afirka da ma wajen nahiyar, kuma ana sa ran Malawi za ta ci babbar gajiya daga taro, kasancewarsa muhimmin dandalin da zai bayar da damar bayyana niyyar kasar ta shawo kan kalubalen da sauye sauyen yawan al’umma ke haifarwa.
Ministan ya kara da cewa, taron zai samar da damar tattaunawa tsakanin masana kimiyya, da masu bincike, da masu tsara manufofi dangane da sauye sauyen da yawan al’umma ke haifarwa. Kana zai taimaka wajen zakulo dabarun warware matsalolin da kasar ke fama da su ta fuskar tsara manufofin tattalin arziki.
Shi ma a nasa bangare, ministan watsa labarai da sauya harkokin kasa zuwa tsarin dijital Moses Kunkuyu, jaddada kalaman mista Banda ya yi, yana mai cewa, Malawi za ta yi amfani da damammakin tattalin arziki na taron, musamman a fannin yawon bude ido, da bunkasa kasuwancin al’ummun kasar. (Saminu Alhassan)