logo

HAUSA

Ayarin motocin fadar shugaban kasar Ghana ya yi hadari

2024-05-20 12:26:20 CMG Hausa

Rahotanni daga kasar Ghana na cewa jerin gwanon motocin shugaban kasar ya gamu da hadari a babbar hanyar Accra zuwa Kumasi, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwar a kalla mutum guda, kuma wata majiya ta ce shugaban kasar ba ya cikin ayarin motocin a lokacin da hadarin ya auku.

Sanarwar da aka fitar game da hakan ta ce hadarin ya auku ne a jiya Lahadi, lokacin da ayarin motocin ke komawa birnin Accra, bayan kammala wasu ayyukan hukuma a karshen mako.

Sanarwar ta kara da cewa, wasu motoci da dama sun yi kaca-kaca, kuma daya daga cikin direbobin motocin ya rasu, yayin da jami’an tsaro da ‘yan sanda dake cikin ayarin masu tsaron shugaban kasar suka jikkata.

Wata kafar watsa labarai ta kasar ta ce wata babbar mota ce ta sha gaban ayarin motocin, wanda hakan ya haifar da mummunan hadarin. (Saminu Alhassan)