logo

HAUSA

Iran ta sanar da rasuwar shugaban kasar da wasu jami’ai a hadarin jirgin sama

2024-05-20 14:31:08 CMG Hausa

 

A yau Litinin, kamfanin dillancin labarai na kasar Iran, da gidan talabijin na kasar sun shaida cewa, shugaban kasar Ebrahim Raisi, da wasu manyan jami’an kasar sun rasu a hadarin jirgin sama mai saukar ungulu dake dauke da su. Mataimakin shugaban kasar Mohsen Mansouri shi ma ya tabbatar da wannan labari a shafinsa na sada zumunta.

Gidan talibijin din kasar ya ce gwamnatin kasar Iran ta kira wani taron ministoci na musamman, inda za a sanar da shirin jana’izarsu. A sa’i daya kuma, gwamnatin ta ba da wata sanarwa ta jimamin rasuwar shugaba Raisi, da ministan harkokin wajen kasar Hossein Amir-Abdollahian da karin wasu manyan jami’ai.

Sanarwar ta ce, gwamnati na tabbatarwa kasar da dukkanin al’ummarta cewa, za a ci gaba da bin hanyar da shugaba Raisi ya zaba, ba kuma wani abu da zai kawo cikas ga harkokin kasar. (Amina Xu)