logo

HAUSA

An bude bikin matasan Sin da Afirka karo na 8 a Beijing

2024-05-20 20:02:50 CMG Hausa

Yau Litinin da safe, aka bude bikin matasan Sin da Afirka karo na takwas, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Ma’aikatar harkokin wajen Sin da asusun Song Qingling na Sin ne suka karbi bakuncinsa tare.

A matsayin wani muhimmin aiki da ya cimma sakamakon dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka, yayin bikin na bana, fitattun wakilan matasa na kasashen Afirka 52 za su dandana al’adun gargajiya da ci gaban Sin, tare da matasa kasar Sin.

Yayin bude bikin, baki mahalarta sun bayyana cewa, Sin da Afirka sun dade suna zaman al'umma mai makomar bai daya. Kuma yayin da ake kan tafarkin zamanantarwa, Sin da Afirka a ko da yaushe suna tafiya tare, kuma suna da makoma guda. Matasan da suka halarci bikin sun kuma bayyana cewa, za su ba da gudummawar hikimar matasa, da gabatar da labarai kan zumunta tsakanin kasar Sin da Afirka yadda ya kamata, da gina kyakkyawar makoma ga dangantakar Sin da Afirka.

Bikin matasan Sin da Afirka na da burin sa kaimi ga yin mu'amala tsakanin matasan Sin da Afirka, da ci gaba da sada dadadden zumuncin dake tsakanin Sin da Afirka, da horas da wadanda za su kara karfafa dangantakar abokantaka ta Sin da Afirka. Kuma daga shekarar 2016 zuwa ta 2023, an gudanar da irin wannan biki cikin nasara har sau bakwai. (Safiyah Ma)